<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Almasihu Yana Nan! LW118</title>
<lyrics>[V1]
 1) Almasihu yana nan!
 Tsoron mutuwa ya ƙare.
 Wannan muka gaskata,
 Ikon kabari banza ne. Halleluya!

[V2]
 2) Almasihu yana nan!
 Ƙofar rai shi ne ya buɗe.
 Mutuwa fa ƙaura ce
 Zuwa rai na har abada. Halleluya!

[V3]
 3) Almasihu yana nan!
 Dominmu ne shi ya mutu.
 Tsarkin zuciya wajib ne
 Ga waɗanda ya fanshe su. Halleluya!

[V4]
 4) Almasihu yana nan!
 Ba mai hana mu ƙaunarsa.
 Ko da rai ko babu shi,
 Mun sa kanmu a hannunsa. Halleluya!

[V5]
 5) Almasihu yana nan!
 Mai sarautar dukan duniya.
 Sai mu bi ta gurbinsa,
 Mu yi mulki cikin Sama. Halleluya!</lyrics>
<hymn_number>118</hymn_number>
</song>